MUSLINCI YA SAMU KARUWA
A kokarin wasu bayin Allah jajirtattu, kamar yadda suka saba wannan karon ma a dai-dai lokacin da ake tsaka da bikin Chrismety su kuma suka shiga aikin Alla wato da'awa,
Alhamdulillah for Today's Outing.....
Yau ranar Christmas, 25 December 2022, mutane 52 ne suka shigo Addinin Musulunci a tawagar da nake, ban San sauran tawagar da bana ciki ba wadanda sun kai tawaga 12.
~ Hakika akwai kalubale akan Musulmi da Musulunci a Arewacin Nigeria, dole Musulmi su tashi su isar da sakon Manzon Allah (S.A.W) Kuma su tsayu wajen karantar da wadanda suka shigo Musulunci, wannan shine babban kalubalen da muke fuskanta bayan shigowar su Musulunci.
~ Aikin yana bukatan kowa da kowa ya shigo ciki ko Kuma ya bayar da gudummuwar sa domin har yanzu akwai kalubale sosai, ba zaka San haka ba sai kana shiga Dazuka, kauyuka da wurare masu zurfi zaka San ana kwashe mutane sosai zuwa cikin wasu addinan da ba Musulunci ba.
~ Kayi iya kokarin ka a lokacin rayuwar ka, kafin Ajali yazo, ko ka mutu yau Allah yasan cewa kayi iya abinda zaka yi.
Amma wallahi abokan zaman mu suna aiki fiye da yadda muke yi, suna da resources ninnkin abinda muke dashi.
Allah ka taimaka mana, ka tayar da wannan addini me haske a zukatan bayin ka.
Comments
Post a Comment